Tallafa wa marayu da marasa ƙarfi zai inganta rayuwar su - Dagacin Garin Ja'en

Dagacin garin Ja'en da ke ƙaramar hukumar Gwale a Kano, Alhaji Isma'il Sa'ad Usman, ya shawarci masu hannu da shuni da ma ƴan ƙungiyoyin ci gaban al'umma, da su ƙara tashi tsaye wajen tallafa wa marayu da abubuwan da su ka sawwaƙa, domin taimaka wa rayuwar su a wannan lokaci na watan azumin Ramadan da ake ciki.
Dagacin ya bayyana hakan ne a yayin taron baiwa yara marayu 71, maza da mata, tallafin kayan Sallah, da su ka haɗar da Yadika da kuma atamfofi, tare da kayan abinci ga iyayen marayun, wanda ƙungiyar Ja'en Facebook Connect, ta basu a ƙofar gidan dagacin Ja'en, a ranar Juma'a 27 ga watan Fabrairu, 2026.
Alhaji Isma'il Sa'ad Usman, ya kuma ce, tallafin da ƙungiyar ta baiwa marayun abin a yaba ne duba da halin ƙuncin rayuwar da ake ciki, a don haka ne ma ya buƙaci sauran jama'a da su yi koyi wajen taimaka wa marayun da ma iyayen su.
Da yake nasa jawabin, shugaban ƙungiyar ta Ja'en Facebook Connect, Auwal Abdullahi Mai Walda, ya ce sun bai wa marayu da iyayen nasu tallafin ne domin rage musu wata damuwa ta yau da kullum.
A cewar sa, "Dama mun saba gabatar da makamancin wannan aikin na alkhairi a duk shekara, kuma za mu ci gaba ba tare da gajiya wa ba, musamman ma fagen duba rayuwar marayu da matasa da masu ƙaramin ƙarfi wajen tallafa musu, in ji Auwal Mai Walda.”
Ya kuma ce, bayan baiwa marayu kayan sallar sun kuma basu kuɗin ɗinki, tare da baiwa iyayensu Shinkafa, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.
Ƙungiyar dai ta Ja'en Facebook Connect, ta kuma sha alwashin ci gaba da taimaka wa marayu da iyayen su, har ma da matasa ta ɓangarori daban-daban domin samar da ci gaban su.
