Hukumar NASENI ta ƙaddamar da na'urar ban ruwa a gona ta zamani mai amfani da hasken rana a Kano.

Hukumar lura da ingancin kimiyya da fasaha ta ƙasa NASENI, ta ƙaddamar da wata na'uarar ban ruwa a gona mai amfani da hasken rana a jihar Kano.
Hukumar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Khalil Sulaiman Halilu, ta ƙaddamar da wannan na'ura ne a ƙananan hukumomin Gabasawa da Kumbotso da ke jihar Kano, a ranar Laraba 2 ga watan Agusta, 2026.
Yayin da yake ƙarin haske akan na'uurar, jam'i'in hukumar bunƙasa noma da raya karkara ta jihar Kano, KNARDA, ya bayyana cewar NASENI ta kawo wannan fasaha ne domin sauƙaƙawa manoma, musamman dangane da batun tattalin arziƙi sakamakon tsadar man fetur da baƙin mai.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, wasu manoma a ƙaramar hukumar Kumbotso sun godewa shugaban hukumar ta NASENI Alhaji Khalil Sulaiman Halilu, bisa yadda ya kawo musu wannan fasaha.
