Koma Labarai
Tattalin Arziki

Dogaro da kai: Hukumar NASENI ta tallafa wa matasa 100 da kekunan ɗinki a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Dogaro da kai: Hukumar NASENI ta tallafa wa matasa 100 da kekunan ɗinki a Kano.

Hukumar lura da ingancin kimiyya da fasaha da ƙere-ƙere ta ƙasa NASENI, ƙarƙashin jagorancin shugaban ta Khalil Sulaiman Halilu, ta raba kyautar kekunan ɗinki guda 100 ga matasa a ƙananan hukumomin Gaya, Ajingi, Albasu da na birnin Kano.

Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin Muhammad Alhassan ya bayyana cewa, sun raba kekunan ɗinkin ne domin matasan su tsaya da ƙafar su.

Ya ce shirin na da nufin bunƙasa tattalin arzƙi da kuma samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

A nasa ɓangaren mai martaba sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya, ya bayyana cewar tallfawa matasan tamkar tallafawa al'umma ne gaba ɗaya.

Da yake nasa jawabin, Shugaban ƙaramar hukumar Gaya Mahmud Tajo Sani, ya godewa hukumar NASENI a madadin ɗaukacin matasan, bisa tallafin da ta basu.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, gabanin baiwa matasan tallafin Kekunan ɗinkin sai da aka basu horo na makwanni shida a kan ɗinki.

Ready to PlayDala FM88.5 FM