Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin ƙaramin ministan kuɗi
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin sabon ƙaramin ministan kuɗi na ƙasar, jim kaɗan bayan da Majalisar dattawa ta tantance shi a matsayin minista a gwamnatin tarayyar ƙasar.
Kafar DCL Hausa ta ruwaito cewa, Shugaba Tinubu, ya amince da naɗinsa a matsayin karamin minista a ma'aikatar kudi ta Nijeriya.
Kafin naɗin nasa a wannan muƙamin shi ne Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin haraji na gwamnatin Najeriya.
