Koma Labarai
Kasuwanci

"Na fahimci cewa Bidiyo na zai iya zama hanyar sauya tunanin mutane" in ji Mutari Hamidu (MK Tecnic):

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
"Na fahimci cewa Bidiyo na zai iya zama hanyar sauya tunanin mutane" in ji Mutari Hamidu (MK Tecnic):

Fitaccen mai ƙirƙirar abun ciki a kafafen sada zumunta, Mutari Hamidu, wanda aka fi sani da MK Tecnic, ya bayyana cewa ya ƙara mayar da hankali kan samar da bidiyoyin ilimantarwa bayan ya fahimci irin tasirin da abubuwan da yake wallafawa ke yi ga masu kallonsa.

MK Tecnic, ya ce a tsawon lokacin da yake ƙirƙirar abun ciki, ya samu saƙonni da dama daga masu bibiyar ayyukansa, inda wasu ke bayyana cewa sun koyi darussa masu amfani daga bidiyoyinsa, lamarin da ya ƙarfafa masa gwiwar ci gaba da wannan salo.

A cewarsa, duk da cewa ba zai iya tantance yawan mutanen da bidiyoyinsa suka yi tasiri a rayuwarsu ba, yana ɗaukar kowace irin amsa da yake samu daga masu kallo a matsayin abin ƙarfafawa.

“Ba zan iya cewa ga adadin mutanen da na sauya wa rayuwa ba. Amma duk lokacin da wani ya sanar da ni cewa wani bidiyo na ya sa ya gyara wani hali ko ya canja yadda yake kallon wani al’amari, hakan yana ba ni ƙwarin gwiwa na ci gaba,” in ji MK Tecnic.

Ya bayyana cewa burinsa shi ne ya ci gaba da samar da bidiyoyin da za su haɗa nishaɗi da ilimantarwa, domin masu kallo su fita da wani darasi mai amfani bayan sun kalli abubuwan da yake wallafawa.

Masu bibiyar ayyukansa sun ce sun fara ganin sauyi a cikin irin saƙonnin da MK Tecnic ke isarwa, inda bidiyoyinsa ke ƙarfafa tunani mai kyau, kyawawan ɗabi’u, da amfani da kafafen sada zumunta ta hanya mai amfani.

MK Tecnic ya ce zai ci gaba da amfani da dandalin da yake da shi wajen ƙarfafa ilimantarwa da wayar da kai, yana mai fatan cewa abun cikin da yake samarwa zai ci gaba da amfani ga masu kallo a sassa daban-daban na ƙasa.

Ready to PlayDala FM88.5 FM