Amfani da kayayyakin da aka ƙirƙira a gida zai bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya - NASENI

Hukumar samar da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙiren cikin gida ta ƙasa NASENI, ta bayyana amfani da kayayyakin da aka kirkira a cikin gida Najeriya a matsayin wani mataki na kawo ci gaban tattalin arziki a faɗin ƙasar.
Shugaban hukumar ta NASENI Khalil Sulaiman Halilu, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro na rabon kayan girki da ya gudana ranar Litinin a birnin Kano.
Khalil Sulaiman Halilu ya bayyana cewar ya zama wajibi al'umma su rungumi kayayyakin da ake samar wa a cikin gida, da sauƙaƙa wa kai tsaye, tare da inganta tattalin arziki.
Da take nata jawabin Ministar kasuwanci da zuba hannun jari Dr. Jumoke Oduwole, ta ya ba da matakin inda ta roƙi waɗanda suka ci gajiyar tsarin da su tafikar da kayayyakin da aka ba su ta hanyar da ya dace
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, sama da mata ɗari biyu ne su ka samu kayan girki da Fanka, da kayan sola waɗanda aka samar a cikin gida Najeriya.

