Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta wanke DCP Abba Kyari kan zarge-zargen da ake yi masa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta wanke DCP Abba Kyari kan zarge-zargen da ake yi masa

Babbar kotun Tarayya ta sallami dakataccen mataimakin kwamishinan 'yansanda Abba Kyari, tare kuma da wanke shi daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.

Mai shari'a James Omotosho ne ya yanke hukuncin kan zarge-zarge 23 da ake yi masa da suka shafi rashin bayyana kadarorinsa, da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar (NDLEA) ta shigar a kan sa wasu shekaru da suka gabata.

An gurfanar da DCP Abba Kyari, ne tare da wasu 'yan'uwansa biyu, waɗanda ake zargin su da yin rantsuwar ƙarya domin yin rufa-rufa wajen ɓoye asalin mamallakin dukiyar.

A zaman na ranar Alhamis 5 ga watan Maris, 2026, a yayin yanke hukuncin, mai shari'a Omotosho ya ce NDLEA, ta kasa gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da zargin da ake yi masa.

Alƙalin ya bayyana cewa ana iya mallakar fili ta hanyar gado ko kyauta da sauran su, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM