Shari'ar tsohon Ministan Shari'a Malami, ta koma hannun sabon alƙali.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Babban alƙalin kotun tarayya, John Tsoho, ya mayar da shari’o’i biyu da EFCC ta shigar kan Abubakar Malami ga Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, wadda ta sanya ranar 27 ga Fabrairu domin fara sauraro.
Matakin ya biyo bayan janyewar Mai Shari’a Obiora Egwuatu daga shari’ar saboda dalilai na ƙashin kai da kuma muradin adalci.
EFCC na tuhumar Malami da laifuffuka 16 da suka shafi badakalar kuɗi, inda ta ce ta gano kadarori da darajarsu ta kai Naira biliyan 212 a Kebbi, Kano da Abuja.
An gurfanar da shi tare da ɗansa da matarsa, amma sun musanta zarge-zargen.
Haka kuma, ana ci gaba da wata shari’a daban da ke gaban kotu kan zargin tallafa wa ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
