Iyaye ku hana ƴaƴan ku roƙon Barka da Sallah don gujewa lalacewar tarbiyyar su - Sheikh Ali Ɗanabba
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya buƙaci iyaye da su hana yaran su roƙon barka da sallah, kasancewar roƙon barka da sallar na buɗewa marasa kirki ƙofar lalata musu yara.
Sheikh Ali Ɗanabba, ya bayyana hakan ne ta shafin sa na sada zumunta a ranar Laraba 17 ga watan Maris, 2026.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake shirin gudanar da ƙaramar sallar idi a gobe Alhamis, ko kuma ranar Juma'a 20 ga watan Maris, 2026.

