Koma Labarai
Tsaro

DSS sun sako Walida, matashiyar da aka sauyawa addini daga Musulunci zuwa Kirista tare da aurar da ita.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya karɓo Walida Abdulhadi Ibrahim, matashiyar da aka ce ta ɓace daga jihar, wadda ke a hannun jami’an DSS.

Gwamnan ya bayyana cewa dukkan batutuwan da suka shafi zargin sace ta za su bi hanyar doka, yana mai jaddada cewa kotuna ne za su yanke hukunci kan lamarin.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a tabbatar da adalci, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati za ta bar doka ta yi aikinta yadda ya kamata.

An dai yi zargin cewa wani jami'in DSS, ne ya sace matashin tare da sauya mata addini, daga Musulunci zuwa Kirista, tare da aurar da ita ga kirista, al'amarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al'umma, bayan da iyayen ta suka koma a kan lamarin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM