Rashin zuwan mataimakin Gwamnan Kano don kare kansa ka iya jawo a tsige shi - Majalisa

Majalisar Dokoki Kano ta bada wa'adin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi a ofishin sa.
Cikin wata sanarwa da majalisar ta karanto a yayin zaman ta na ranar Alhamis 5 ga watan Maris, 2026, ta ce ana zargin mataimakin gwamnan da salwantar da kuɗaɗe a ofishin sa, inda ta bashi mako biyu domin zuwa ya kare kan sa.
Da yake ƙarin bayani shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Lawan Husaini Dala, ya ce rashin bayyanar sa gaban majalisar domin kare kan sa, ka iya sanya wa a tsige shi daga kan kujerar sa.
A cewar sa, "Laifukan da ake zargin Aminu Gwarzo, sun haɗar da albazzazaranci da salwantar da kudaɗe ba bisa ƙa'ida ba na gwamnati, kuma za a kai masa takardar wa'adin zargin domin ya zo majalisar nan da mako biyu ya kare kansa, in ji shi.”
Ya ci gaba da cewa, za a dawo da takardar gaban majalisar domin a duba amsar da mataimakin gwamnan ya bayar, idan ba a gamsu ba kuma za a ci gaba da kuɗiri na tsige shi daga kan kujerar sa.
A cewar sanarwar ta samu sahalewa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ce, sanya hannun ƴan majalisar dokokin jihar Kano guda 38, su ka amince domin a sanar da shi, domin gabatar masa da zarge-zargen da ake yi masa.

