Koma Labarai
Addini

Iyaye ku rinƙa sanya ƴaƴanku mata a gaba yayin zuwa sallar Tuhajjudi don gujewa gurɓacewar tarbiyyar su - Hukumar Shari'a a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Iyaye ku rinƙa sanya ƴaƴanku mata a gaba yayin zuwa sallar Tuhajjudi don gujewa gurɓacewar tarbiyyar su - Hukumar Shari'a a Kano

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta shawarci iyaye da su rinƙa sanya ƴaƴansu ƴan mata a gaba yayin zuwa sallar dare ta Tuhajjudi, domin gujewa saɓawa hanya su haɗu da ɓata garin samari wanda hakan ka iya janyo gurɓacewar tarbiyyar su.

Sheikh Ali Ɗanabba, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, ya kuma buƙaci ƴan mata da samari suji tsoron Allah, idan za su je sallar su rinƙa yin abinda ya kamata tare da dagewa da addu'o'i.

Sheikh Ɗan Abba, ya kuma ce akwai buƙatar limamai su lura da ƙarar amsa kuwar masallatan da suke jan sallar dare ta Tuhajjudi, domin gujewa rinƙa takurawa masu wani uziri a gida da ƙarar amsa kuwwar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM