Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta yankewa "Mai Siket” hukuncin shekaru 20 kan yi wa tsohuwa mai shekaru 85 Fyaɗe a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta yankewa "Mai Siket” hukuncin shekaru 20 kan yi wa tsohuwa mai shekaru 85 Fyaɗe a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano ƙarkashin jagorancin A'isha Mahmoud, ta yanke wa wani mutum Muhammad Zulfalalu, wanda aka fi sani da “Mai Siket”, hukuncin shekaru 20 a gidan yari bayan samunsa da laifin yi wa wata tsohuwa mai shekaru 85 fyade a Karamar Hukumar Kiru ta jihar Kano.

Mai shari’ar ta yanke wa mutumin hukuncin ne bayan ta tabbatar cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifukan da ake tuhumarsa da su ba tare da wata shakka ba.

Kotun ta kuma same shi da laifuka tara da suka haɗar da fyade da shiga gida ba bisa ka’ida ba.

An yanke masa hukuncin shekaru 20 kan laifin fyade da karin shekaru shida kan laifin shiga gida da ƙarfi, amma hukuncin zai gudana lokaci guda.

Haka kuma, kotun ta umarce shi da biya diyyar naira 500,000 ga wadda abin ya shafa.

Mai gabatar da kara, Aisha Adamu, ta bayyana cewa laifukan sun faru tsakanin watan Agustan 2019 da Yunin 2020 a Gidan Kwano, Kwanar Ɗangora da ke Karamar Hukumar Kiru a Kano, ta ce wanda aka yankewa hukuncin ya shiga gidan matar cikin dare tare da yi mata fyade.

Bayan hukuncin, Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Maude (SAN), ya bayyana cewa hukuncin wata babbar nasara ce a ƙoƙarin gwamnati na yaƙi da cin zarafi da tashin hankali da ake yi wa mata da sauran masu rauni a cikin al’umma.

Ready to PlayDala FM88.5 FM