Kotu ta aike da Usman Hassan gidan yari kan zargin kashe Kabiru Isyaku, bayan yi masa fashi da makamin babur na roba-roba a Kano.

Kotun majistret mai lamba 53, a Kano, ta aike da wani matashi Usman Hassan gidan ajiya da gyaran hali, bisa zargin sa da laifin haɗa baki da kisan kai.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar Usman Hassan ya haɗa baki da wasu matasa biyu inda suka yi wa wani matashi mai suna Kabiru Isyaku fashi da makamin babur ɗin na na roba-roba, inda suka kuma sassari matashin har sai da rai ya rasu.
Yayin da aka karanta kunshin zargin mai gabatar da ƙara ya bayyana cewar, kotun ba ta da hurumin sauraren shari'ar kisan kai.
Sauran waɗanda ake zargin sun haɗar da Dan Amira da Abba Thomas, dukkansu mazauna Ɗan dinshe sai dai mutane biyun sun tsere.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Kotun ta aike da Usman Hassan gidan gyaran hali domin jiran shawarar lauyoyin gwamnati a kan shari'ar.



