Kotu ta bada belin lauya kan zargin yaɗa labarin ƙanzon kurege da buga takardun bogi a Kano.

Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa NBA, reshen jihar Kano, wato Kano State Branch, ta yi wa kotun majistret mai lamba 9 tsinke.
Tun da farko yansanda ne suka gurfanar da wani lauya mai suna Hamisu Ɗandago, bisa zargin sa da laifin buga takardar jabu da yaɗa labarin kanzon kurege.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar, lauyan ya rubuta takarda da sunan wani kamfani ya kai wata kotu domin janye wata Shari'a, sai dai ya musanta zargin.
A yayin zaman kotun na yau Talata 29 ga watan Satumban 2026, lauyan da yake kare shi Barrister Danjuma Hussaini, ya roƙi kotun da ta sanya shi a hannun beli.
Lauyar gwamnati Barrister A'isha Bashir minjibir bata yi suka ba.
Mai Shari'a Haulatu Magaji Kankarofi, ta sanya shi a hannun beli a bisa sharaɗin idan ya tsere masu karɓar belin za su biya dubu ɗari biyar.
Bayan fitowa daga kotun ne, Mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi ta ƙasa NBA, reshen jahar Kano, Barrister Ahmad mai yaƙi, ya bayyana cewar sun je kotun ne domin tabbatar da adalci.
Barista Ahmad Mai yaƙi ya kuma ce, zuwan nasu ba zai kawo tangarda ga bincike ba kuma duk lauyan da aka samu da laifi ƙungiyar za ta hukunta shi.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, sama da lauyoyi hamsin ne suka je kotun karkashin jagorancin shugaban kungiyar su na jahar Kano.



