Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta wanke Yusif Nadabo kan zargin kashe matarsa a jihar Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta wanke Yusif Nadabo kan zargin kashe matarsa a jihar Kano.

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11 da ke zaman ta a Bompai, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu, ta sallami wani magidanci mai suna Yusuf Nadabo Kawule, wanda ake zargi da kashe matarsa.

An gurfanar da Yusuf ne bisa zargin kisan kai, wanda ya saɓa da sashe na 221 na dokar laifuka, amma ya musanta tuhumar.

A yayin zaman shari’ar na ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba, 2026, lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidunsu, yayin da wanda ake tuhuma shi ma ya gabatar da bayaninsa a gaban kotu.

Kotun ta yanke hukuncin sallamarsa ne bisa rashin gamsassun hujjoji da shaidu da za su tabbatar da zargin da ake yi masa.

Lamarin ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo da ke Karamar Hukumar Takai, inda ake zargin ya ɗauki marigayiyar a babur domin nema mata gida a wani ƙauye, amma suka yi hatsari a kan hanya, wanda ya yi sanadin rasuwarta.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kama Yusuf tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Wakilinmu Aminu Abdu Baka Noma, ya rawaito cewa, kotun ta sallami mutumin ne bayan kammala sauraron shari’ar.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM