Kotu na daf da yanke hukunci kan matasan da ake zargi da kashe matar aure da ƴaƴan ta shida a Chiranchi, Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 17 views

Rahotanni sun bayyana cewa, yanzu haka ana daf da fara hukunci a kan matasan nan da ake zarginsu da kashe matar auren nan da ƴaƴanta shida a Unguwar Ciranchi da ke yankin Ɗorayi, a Kano.
Yanzu haka dai lauyoyin gwamnatin Kano sun isa Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11, a dai-dai lokacin da ake shirin yanke wa matasan hukuncin.
Mu na tafe da ƙarin bayani.



