Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta tilasta wani ɗan TikTok sharewa da tsaftace harabar hukumar Karota, a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta tilasta wani ɗan TikTok sharewa da tsaftace harabar hukumar Karota, a Kano.

‎Wata kotun majistare a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali, ta yanke wa ɗan TikTok, Rabi’u Sani Zage, hukuncin aikin tilas na makonni biyu ba tare da tsare shi a gidan yari ba.

Hukuncin na zuwa ne bayan samunsa da laifin ɓata sunan ma’aikatan hukumar KAROTA.

‎A yayin zaman hukuncin, kotun ta umarci matashin da ya riƙa sharewa da tsaftace harabar hedikwatar KAROTA da ke Club Road, Kano, ko kuma gudanar da duk wani aikin hidima da hukumar za ta ba shi.

‎Haka kuma, an umarce matashin da rubuta takardar neman afuwa ga shugabancin hukumar, tare da alƙawarin cewa ba zai sake aikata irin wannan laifi ba.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM