Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta tsare Hajara Sani da mutane 2 bisa zargin kashe wani yaro bayan garkuwa da shi a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta tsare Hajara Sani da mutane 2 bisa zargin kashe wani yaro bayan garkuwa da shi a Kano.

Babbar kotun jiha Mai lamba 13 ta aike da wasu mutane gidan gyaran hali bisa zarginsu da kashe wani yaro bayan Garkuwa da shi a Kano.

An gurfanar da Hajara Sani da Hayatullah Armayau dakuma Jibrin Ado dauke da takardar tuhume tuhumen hadin Baki domin aikata laifi da Garkuwa da mutane da kuma kisan Kai.

Lauyan gwamnati Barista Lamido Abba Soran dinki tare da Barista Iliyasu Ibrahim sune suka gabatar da mutanen a kotun.

A yayin zaman, bayan karanto musu tuhume-tuhumen sun Musanta.

Ana zargin Hajara Sani Wadda take aiki a gidansu marigayi da dauke Aliyu Haidar kuma takaiwa Hayatullah da kuma Jibrin kuma ake zargin sun hada Kai suka nemi kudin fansa har naira Miliyan biyu, amma sakamakon hanasu suka hallaka Yaran.

Ƙunshin zargin ya ayyana cewa, lamarin ya faru ne a kauyan Gobirawa da ke karamar hukumar Rano.

Kotun kuma ta Aike dasu gidan gyaran hali har zuwa Ranar 4 ga watam Disamba na 2026, domin Fara Jin shaidu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM