Malam Lawan Triumph ya yi ƙarar wani lauya bisa zargin sa da ɓata masa suna a Kano.

Kotun majistret mai lamba 53 ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Jamilu Dayyabu Haruna, ta sanya ranar 28 ga watan Oktoba, 2026, domin ci gaba da sauraron wata Shari'a wadda Mallam Lawan Abubakar Triumph ya shigar, yana ƙarar Barrister Hashim Hussaini Hashim bisa zargin ɓata suna.
Mai ƙarar ta bakin lauyan sa Barrister Abdurrazak Ahmad ya bayyana cewar, wanda ake ƙara ya ɓata sunan Mallam Lawan ta dandalin sada zumunta na Facebook.
A zaman kotun na ranar Alhamis 22 ga watan Oktoba, 2026, lauyan mai ƙara ya zo kotun sai dai wanda ake ƙara bai zo ba.
Kotun ta tambayi masinja ko an sanar da wanda ake ƙara da sammace, inda ya bayyana cewar an sadar da shi sai dai an sanya hannun wata mata da sunan ta wanda ya saɓa da sunan wanda ake ƙara.
Daga nan ne lauyan mai ƙara ya roƙi kotun da a sadar da sammacen ta hanyar turawa ta Whattapp, da kuma liƙawa a ƙofar gidan wanda ake ƙara, inda nan take kotun ta amince da roƙon.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Kotun ta kuma sanya ranar 28 ga wannan wata na Octoba, 2026, domon ci gaba da sauraron shari'ar.



