Koma Labarai
Shari'a

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta yanke wa Umar da Yakubu hukuncin kisa bayan samun su da laifin kashe Fatima da ƴaƴanta 6 a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 41 views
Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta yanke wa Umar da Yakubu hukuncin kisa bayan samun su da laifin kashe Fatima da ƴaƴanta 6 a Kano.

Babbar kotun jaha mai zaman ta a Bompai ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Nasir Saminu, ta zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu mutane biyu da suka haɗar da Umar Auwal da Yakubu Dayyabu, samun su da laifin kashe matar auren nan Fatima Abubakar, da ƴaƴan ta shida a unguwar Chiranchi da ke yankin Ɗorayi.

Kotun ta yanke hukuncin ne a yayin zaman ta na ranar Juma'a 6 ga watan Nuwamba, 2026.

Kotun ta kuma wanke Isyaku Yakubu dangane da tuhumar bisa rashin samun sa da laifi.

Gwamnatin jahar Kano ce dai ta gurfanar da mutanen a gaban kotun, a kan tuhumar.

Kotun ta kuma ƙara yi wa mutanen biyu ɗaurin rai da rai a tuhumar haɗa baki yayin da ake dakon hukunci a tuhumar kisan kai a unguwar Tudun Yola da kwarin barka a ranar 11 ga wannan wata na Nuwamba, 2026, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM