Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta aike da Barrister Ɗalhatu Shehu Usman gidan gyaran hali a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 45 views
Kotu ta aike da Barrister Ɗalhatu Shehu Usman gidan gyaran hali a Kano.

Babbar kotun jaha mai zaman ta a Miller road ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Zuwaira Yusuf, ta aike da lauyan nan mai zaman kansa a Kano, Barista Ɗalhatu Shehu Usman gidan ajiya da gyaran hali.

An gurfanar da lauyan a gaban kotun sai dai lauyoyin sa sun yi suka akan rashin hurumi akan masu gabatar da kara, inda suka shaidawa kotun cewar a bisa doka lauyoyin gwamnati ne suke gabatar da hurumin ƙara ba lauyoyi masu zaman kansu ba.

Kotun ta waiwayi lauyoyi masu gabatar da kara inda suka bayyana wa kotun cewar, babban baturen Shari'a na jahar Kano ne ya lamunce musu su gabatar da ƙara a wannan Shari'ar.

Bayan tafka muhawara ne daga nan kotun ta ayyana ranar juma'a a matsayin ranar da za ta bayyana matsayarta akan ko waɗannan lauyoyi suna da hurumi ko akasin hakan.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewar, gwamnatin jaha ce ta gurfanar da lauyan mai suna Barrister Ɗalhatu Shehu Usman a kotun, sai dai ba a karanta tuhumar ba har sai kotun ta bayyana matsayarta.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM