Jam'iyyar NDC ta maka INEC a kotu kan cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo

Jam’iyyar NDC ta shigar da ƙara a kotun tarayya da ke Abuja, tana neman a tilasta wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) mayar da sunan ɗan takararta na gwamnan Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, cikin jerin sunayen ’yan takarar zaɓe.
Matakin ya biyo bayan rashin bayyana sunan Gwarzo a jerin sunayen da INEC ta fitar, duk da cewa jam’iyyar ta ce ɗan takararta ya cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata domin tsayawa takara.
Jigon jam’iyyar NDC Kwankwasiyya, Dr. Yusuf Kofarmata, ne ya bayyana shigar da ƙarar, inda ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar su ci gaba da yaƙin neman zaɓe da addu’o’i, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.
Kofarmata ya ce suna fatan kotu za ta yanke hukuncin da zai baiwa Gwarzo damar shiga takarar gwamnan jihar Kano.



