Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta tsare malamin nan Sheikh Halifa a gidan yari kan zargin karkatar da 34,875,000 a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta tsare malamin nan Sheikh Halifa a gidan yari kan zargin karkatar da 34,875,000 a Kano.

Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare malamin nan Sheikh Halifa Abdulmajid Nazifi a gidan yari bayan Hukumar EFCC ta gurfanar da shi bisa zargin karkatar da ₦34,875,000.

Kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Hukumar EFCC ta fitar a shafin ta na sada zumunta a ranar Alhamis 15 ga watan Oktoba, 2026.

Sanarwar ta ce an gurfanar da Sheikh Abdulmajid a gaban Mai Shari’a Musa Karaye ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, inda hukumar ta zarge shi da karkatar da kuɗin Fahad Balarabe Adaji da aka tura domin sayen taliyar IRS Spaghetti daga BUA tsakanin Satumba da Oktoba, 2024.

EFCC ta ce Sheikh Abdulmajid ya musanta tuhumar da ake masa, inda lauyan hukumar, Mustapha Maiwada, ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari’a tare da bayar da umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali.

Kotun ta bayar da umarnin tsare malamin a gidan gyaran halin tare da ɗage shari’ar zuwa 2 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM