Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta fara sauraron shaida kan zargin yanke wa Ashiru Sani maƙarfafa a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta fara sauraron shaida kan zargin yanke wa Ashiru Sani maƙarfafa a Kano.

Babbar kotun jiha mai lamba ɗaya da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako, Kano, ta fara sauraron shaida dangane da tuhumar da ake yi wa Maimuna Idris, sakamakon zargin ta da yanke wa saurayin ta Ashiru Sani maƙarfafa.

A zaman kotun na yau, mai gabatar da kara Barista Safiya Yalwati Yahaya, ta gabatar da shaidar ta wato Shi wanda abin ya faru akansa, inda yai bayani dalla dalla kan yadda abin ya faru.

Ya bayyana cewar ta shayar da shi ƙwayar Diyaza hakan ya sa ya rabu da hankalin sa, daga bisani ta aikata masa wannan ɗanyan aiki.

Bayan kammala jin shaidar kotun ta sallame shi kuma ta sanya ranar 19/11/2026 domin cigaba da shari'ar.

Tunda fari dai ana zargin Maimuna Idris da Yanke makarfafar Ashiru Sani, a wani ɗakin hutawa, hakan ya sa aka gurfanar da ita a kotun amma ta musanta tuhumar da ake yi mata.

Bayan fitowa daga Kotun ne wakilinmu Aminu Abdu Bakanoma, ya zanta da matashin da aka yanke wa maƙarfafa Ashiru Sani, wanda ya bayyana damuwar sa kan halin da yake ciki, inda ya roƙi al'umma da a taimaka masa wajan samun kudin aikin da za a yi masa.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM