Koma Labarai
Shari'a

Kotun ta yi umarnin a rataye wani magidanci bisa samun sa da laifi a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotun ta yi umarnin a rataye wani magidanci bisa samun sa da laifi a Kano.

Babbar Kotun jihar Kano, mai lamba 15 ƙarƙashin Mai sharia Sanusi Ado Ma'aji, ta yanke wa Hamisu Baita Mai gyaran mukulli hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Da yake yanke hukuncin, mai shari'ar ya ce kotun ta gamsu da shedun masu gabatar da ƙara, bayan da Lauyan gwamnnati Barista Ummi lawal Tudun wada, da Barista Bello Isa Lawan suka gabatar da shaidu shida.

Sai dai lauyan mutumin Barista Mubarak Abubakar ya gabatar da Hamisu Baita inda ya Kare kansa tare da gabatar da sheda daya Kotun tayi watsi da Karen kansa da ya yi.

Tun da farko, a shekarar 2024 a unguwar Dandago filin mushe akayi zargin Hamisu Baita Mai gyaran mukulli ya kashe Suwudi Surajo Dan shekaru 5 bayan ya yankeshi tare da kwakule masa Idanu.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM