Kotu ta yi watsi da ƙarar wanda ake zargi da barazanar yaɗa hotuna da bidiyon tsaraicin Gwamnan Kano.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan Sanusi Dankaka, wanda ake zargi da barazanar yaɗa hotuna da bidiyoyin tsiraici da aka ce na Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne a shafinsa na Facebook.
Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan lauyan masu gabatar da ƙara, A.Y. Afegbua, ya nemi kotun ta ba su damar janye ƙarar.
A yayin zaman kotun na ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba, 2026, lauyan wanda ake tuhuma, Ƙauna Penzin, bai nuna adawa da buƙatar ba, lamarin da ya sa alƙalin ya amince da janye ƙarar tare da yin watsi da ita.
Tun da farko, kotun ta sanya ranar 7 ga Disamba domin fara sauraron shari’ar, bayan Dankaka ya musanta zargin da ake masa.
Sai dai daga bisani aka dawo da shari’ar cikin jerin ƙararrakin da kotun za ta saurara a ranar Talata, inda masu gabatar da ƙara suka nemi janye ta.
Majiyar labarin ta ruwaito cewa, hukuncin ya kawo ƙarshen wannan ƙara a kotun, ba tare da an gudanar da cikakken sauraron shaidu ko yanke hukunci kan sahihancin zarge-zargen ba.



