Kotu ta tsare Uwar gida kan zargin kashe amarya don ta haifi ɗa namiji a Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun majistret mai lamba 2 ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Auwal Yusuf Sulaiman, ta aike da wata mata gidan gyaran hali bisa zargin ta da kashe kishiyar ta.
Ana zargin Safiya Hussaini da laifin kashe amaryar ta hanyar daddatsata da adda, don kawai ta haifi ɗa namiji duk da cewar itama uwar gidan ta haifi ɗa namiji kwanaki biyar kafin haihuwar amaryar.
A yayin zaman kotun na ranar Laraba 30 ga watan Satumban 2026, an karanta mata zargin sai dai ba aji martanin ta ba, kasancewar kotun ba ta da hurumin sauraren shari'ar kisan kai.
Kotun ta umarci lauyoyin gwamnati da su fitar da shawara domin ɗaukar mataki na gaba.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, laifin da ake tuhumar matar ya saɓa da sashi na 221 na kundin penal code.



