Kotu ta yanke wa wasu ma'aikatan kamfani hukuncin shekaru 7 kan karkatar da miliyan 58 a Kano

Kotun majistare mai lamba uku da ke Gyadi-Gyadi a Kano, ta yanke wa Abubakar Adamu da Salmanu Magaji hukuncin ɗaurin shekaru bakwai, bayan samun su da laifin karkatar da kuɗin kamfanin Muwaffak Global har naira miliyan 58.
A hukuncin da mai shari’a Rakiya Lami Sani ta yanke, kotun ta ɗaure su shekaru biyu ko tarar naira dubu 500 kan haɗa baki domin aikata laifi. Ta kuma yanke musu ɗaurin shekaru biyar ba tare da zaɓin tara ba kan zamba cikin aminci.
Mai kamfanin da ke Kantin Kwari, Alhaji Gazzali Ahmad, ne ya kai ƙarar mutanen biyu, waɗanda suka kasance manaja da mataimakinsa. Ya zarge su da karkatar da kuɗin kamfanin ta hanyar buɗe wani asusun banki daban, lamarin da ya kai ga gurfanar da su.
Kotun ta kuma umarce su da su mayar da naira miliyan 58 ɗin cikin watanni shida, tare da sanar da su cewa, suna da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 30 daga ranar yanke hukuncin idan ba su gamsu ba.



