Koma Labarai
Shari'a

Babbar Kotun Kano ta tsare Ali Sulaiman Gadon Ƙaya kan zargin kashe matarsa Maryam Nababa Badamasi

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Babbar Kotun Kano ta tsare Ali Sulaiman Gadon Ƙaya kan zargin kashe matarsa Maryam Nababa Badamasi

Babbar Kotun jaha mai lamba 15, ta fara sauraron wata ƙara wadda gwamnatin jaha ta gurfanar Ali Sulaiamn Adam Gadon Ƙaya, bisa zargin sa da laifin kashe matarsa Maryam Nababa Badamasi.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar bayan ya kashe ta ya kuma cinnawa ɗakinta wuta.

A zaman kotun na ranar Alhamis 16 ga Yuli, 2026, yayin da aka karanta masa zarge-zargen da ake yi masa a kotun ya musanta.

Lauyan gwamnati Lamiɗo Abba Soronɗinki, ya roƙi kotun da ta ba shi wata rana domin gabatar da shaidu a kan shari'ar.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il, ya zanta da lauyan gwamnati Lamiɗo Abba Soronɗinki, wanda ya bayyana cewar sun shirya tsaf don fara gabatar da shaidu.

Kotun ta sanya ranar 27 ga wannan watan don bayyana matsayar ta a kan roƙon beli da lauyan kariya ya yi.

Ready to PlayDala FM88.5 FM