Matashi Umar Auwalu ya ce shi kaɗai ya kashe ƙanwar mahaifinsa da ƴaƴan ta 6 a Ɗorayi Chiranchi da ke Kano

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ta 11, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta ci gaba da sauraron shaidun kariya a shari’ar da ake yi wa Umar Auwalu, Isyaku Yakubu da Yakubu Ɗayyabu.
Yayin da yake kare kansa a gaban kotu, Umar Auwalu ya bayyana cewa shi kaɗai ne ya kashe kanwar babansa da ‘ya’yanta shida a unguwar Ciranci.
Ya kuma shaida wa kotun cewa wani boka mai suna Tomas ne ya ba shi turare tare da umartarsa da ya ci gaba da aikata irin waɗannan laifuka.
Umar ya ƙara da cewa Isyaku Yakubu Chobe da Yakubu Dayyabu ba su da hannu a lamarin, yana mai cewa ya ambaci sunayensu ne bayan wahalhalun da ya ce ya sha a hannun ’yan sanda bayan kama shi.
A zaman kotun na ranar Laraba 15 ga Yuli, 2026, lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin Barista Safiya Yalwati da Barista Zaharaddeen Hamisu Kofar Mata sun gabatar da jami’in ɗan sanda mai bincike, Kofural Aliyu Jamilu, yayin da lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma suka gabatar da shaidun kariya.
Mai Shari’a Nasiru Saminu ya ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yuli, 2026.



