Kotu ta yanke wa Tahir Mahmud hukuncin kisa bisa samun sa da laifin kashe Shamsu Yakubu kan musun siyasa a Kano.

Babbar Kotun jahar Kano, mai lamba 5 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a A'isha Mahmud, ta ayyana hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani matashi mai suna Tahir Tanimu, bisa samun sa da laifin haɗa baki da kisan kai.
A zaman kotun na ranar Litinin 3 ga Agusta, 2026, Lauyan gwamnati Lamido soron ɗinki ya bayyana wa kotun cewar, a ranar 2 ga watan Agusta, 2023, Tahir Tanimu sun haɗa baki da Joseph Matin sun kashe wani matashi mai suna Shamsu Yakubu, sakamakon musun siyasa.
Barrister Lamido soron ɗinki, ya gabatar da shaidu huɗu a gaban kotun, inda waɗanda ake zargin suka kare kansu.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta yi watsi da shaidun kariya inda aka gamsu da shaidun mai gabatar da ƙara.
Kotun ta ayyana hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Tahir Tanimu mai shekaru 31, yayin da shi kuma Joseph Matin ɗan shekaru 15 aka ayyana cewar an bar shi a ƙarƙashin kulawar gwamnati kasancewar shekarunsa 15 lokacin da aka aikata laifin.



