An sake gabatar da Umar Faruk a kotu kan zargin kashe matashi Nura Aliyu a Kano.

Babbar Kotun jahar Kano mai lamba 26 ƙarƙashin jagorancin mai Shari'a Hanif Sanusi Chiroma, ta sanya ranar 31 ga wannan watan don bayyana matsayar ta akan rokon beli da aka yi dangane da wata Shari'a.
Gwamnatin jahar Kano ce dai ta gurfanar da wani mutum mai suna Umar Faruk bisa zargin haɗa baki da kisan kai.
Ƙunshi zargin ya bayyana cewar, a ranar 21 ga watan Yuni 2025, wanda ake tuhuma Umar Faruk sun hada baki da wani abokin sa sun kashe wani matashi mai suna Nura Aliyu.
Tuhumar da ake yi wa Umar Faruk, ta saɓa da sashe na 21 na kundun Final code.
A zaman kotun na ranar Laraba 29 ga Yuli, 2026, wanda ake tuhuma ya musanta zargin da ake yi masa a kotun.
Lauyan sa ya roƙi kotun da ta sanya shi a hannun beli, sai dai lauyoyin gwamnati sun yi suka, a nan ne kotun ta sanya rana domin bayyana matsayarta.



