Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta yanke wa amarya Saudat hukuncin kisa kan samunta da laifin kashe angon ta kwanaki 9 da aurensu a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta yanke wa amarya Saudat hukuncin kisa kan samunta da laifin kashe angon ta kwanaki 9 da aurensu a Kano

Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Maryam Sabo, ta yanke wa amaryar nan Saudat Jibril hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris, kwanaki tara da aurensu.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan sauraron shaidun ɓangarorin biyu a kan shari'ar.

Lamarin ya faru ne a watan Mayun 2025, a unguwar Farawa da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, bayan ma’auratan sun yi kwanaki tara da aure.

Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya gabatar da shaidu uku, yayin da lauyan wadda ake ƙara, Barista Abdulfatah Muhammad, ya gabatar da Saudat Jibril domin kare kanta.

Mai Shari’a Maryam Sabo ce ta jagoranci zaman, inda kotun ta amince da shaidun masu gabatar da ƙara tare da yin watsi da bayanan da Saudat ta gabatar domin kare kanta.

Bayan yanke hukuncin, jami’an gidan yari suka tafi da ita, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM