Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar lauyoyi NBA reshen Kano, sun yi wa kotu tsinke sakamakon gurfanar da wani lauya a kotun.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa NBA reshen jihar Kano, sun yi wa kotun majistret mai lamba 9 tsinke sakamakon gurfanar da wani lauya a gaban kotun.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, yanzu haka dai ana shirye-shiryen karantawa lauyan tuhumar da ake yi masa a gaban kotun.
Tunda fari dai rundunar ƴan sanda ne na shiyya ta ɗaya (Zone One) suka gurfanar da lauyan a gaban kotun.
Mu na tafe da ƙarin bayani akai.



