Koma Labarai
Shari'a

Zargin Kisa: Kotu ta sake aikewa da ƴar TikTok Fatima gidan gyaran hali a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Zargin Kisa: Kotu ta sake aikewa da ƴar TikTok Fatima gidan gyaran hali a Kano.

Kotun majistret mai lamba 2 da ke Kano, karkashin jagorancin mai Shari'a Auwal Yusuf Sulaiman, ta sake aikewa da Fatima Abdullahi, gidan gyaran hali bisa zargin kashe saurayinta ta hanyar ƙona shi da wuta.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar Fatima Abdullahi wadda ta ke zaune a unguwar Kuntau a Kano, ta kashe saurayin ta a cikin ɗakinta daga nan ta cinnawa kanta wuta don ta ɓoye sawun bincike, sai dai yansanda sun gano raunika a kansa a yayin gudanar da bincike.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewa, ana jiran shawarar lauyoyin gwamnati domin ɗaukar mataki na gaba.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM