Kotu ta tsare matasa biyu bisa zargin su da laifin kashe wata dattijuwa kan zargin ta da Maita a Kano

Kotun majistret mai lamba 25, ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Usman Adamu, ta aike da wasu matasa biyu gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin su da laifin kisan kai.
Ƙunshin zargin ya bayyana cewar a ranar 30/6/2026, wani mutum mai suna Abdullahi Hamza ya je caji ofis ɗin yansanda ya shigar da ƙara, a kan cewar wasu mata biyu ƴan uwa da suka haɗa da Zulaidaini Uba, da Marwiyya Uba, sun haɗa baki sun kashe wata mata mai suna Fatima Abdullahi yar kimanin shekaru 60, mazauniyar Ƙauyen Kwakumeri da ke Ƙaramar Hukumar Takai, a kan zargin maita.
Lokacin da aka karanta musu ƙunshin tuhumar mai gabatar da kara ya bayyana cewar, kotun ba ta da hurumin sauraren shari'ar kisan kai sai an jira shawarar lauyoyin gwamnati.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, Kotun ta aike da matasan gidan gyaran hali an kuma sanya makonni biyu domin a ƙara gabatar da su.



