Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta yi watsi da buƙatar cire rubutun Arabic a jikin kakin sojin Najeriya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta yi watsi da buƙatar cire rubutun Arabic a jikin kakin sojin Najeriya

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Lagos, ta yi watsi da ƙarar da aka shigar a gabanta da ke neman cire rubutun Arabic daga kayan Sojojin Najeriya.

Kotun ta yanke hukuncin a zaman ta na ranar Laraba 15 ga Yuli, 2026, kamar yadda kafar RFI Hausa ta ruwaito.

Kotun ta ce wani mutum guda bashi da hurumin wakiltar kafatanin ƴan ƙasar wajen neman a cire rubutun Arabic ɗin daga tambarin sojojin Najeriya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM