Koma Labarai
Addini

Idan aka soya naman sallah a fito dashi a taimaka wa gwagware, da mabuƙata - Sheikh Ali Ɗanabba

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Idan aka soya naman sallah a fito dashi a taimaka wa gwagware, da mabuƙata - Sheikh Ali Ɗanabba

Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya bayyana cewa akwai buƙatar duk wanda Allah ya horewa yin Layyah, ya soya naman, ya fito da naman waje domin taimaka wa gwagware da sauran masu ƙaramin ƙarfi.

Sheikh Ali Ɗan Abba, ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, yau Laraba, daga ƙasa mai tsarki.

Ya shawarci al'ummar Musulmi da cewar, duk wanda Allah ya baiwa dama, to ya yanka dabbar da ta dace domin yin Layyah, don samun ladan da ake samu.

Ya kuma ce akwai buƙatar duk wanda ya samu damar yin Layyah, ya raba naman kamar yadda sunnar Ma'aiki ta nuna, a kyautar da wani a kuma yi sadaka, tare da barin wanda za su yi amfani da shi a gida.

A cewar sa, "Ya kamata jama'a su dage da yin Kabarbari a cikin ranakun babbar sallar nan, tare da sada zumunci domin rabauta da rahamar Ubangiji maɗaukakin Sarki, in ji shi.”

Sheikh Ali Ɗanabba, ya kuma buƙaci a taimaka wa waɗanda basu samu damar yin Layyah ba da nama, ka da a busawa mutane ƙamshin nama a bar su haka, don haka idan aka soya a fito dashi waje a taimaka wa waɗanda ba su yi ba.

Ready to PlayDala FM88.5 FM