Doka za ta yi aiki a kan duk wanda ya buɗe masallacin juma'a a Kano ba da neman izini ba - Hukumar Shari'a

Hukumar Shari'a ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta ce ba za ta lamunci yadda wasu suke yin gaban kai wajen buɗe masallatan Juma'a ba tare da neman izinin ta, tana mai cewa duk wanda aka samu da wannan laifi doka za ta yi aiki a kansa.
Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da gudanar a ofishin sa, a ranar Juma'a 10 ga Yuli, 2026.
Ya ce a dokar da ta kafa hukumar, doka ta hudu sashi na shida, ya bayyana cewa mutum ba zai je ya gina Masallacin Juma'a ba har sai ya je hukumar ya nemi izini, amma duk da hakan wasu suke bujire wa lamarin.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya'u ya ruwaito cewa, Sheikh Ali ya kuma ce hukumar na buƙatar duk wanda yake son zai gina masallacin juma'a to ya bi hanyoyin da suka dace domin neman izini saboda gudun taka doka.
A ƙarshe Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma nemi waɗanda suke karya doka wajen bude masallacin juma'a, ko ɗaga likkafar masallaci daga Kamsul-Salawati zuwa na Juma'a ba tare da neman izina ba, da su daina, domin gujewa fuskantar hukunci.


