Koma Labarai
Addini

Hajji 2026: Najeriya ta kammala jigilar maniyyatan ta zuwa ƙasar Saudiyya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hajji 2026: Najeriya ta kammala jigilar maniyyatan ta zuwa ƙasar Saudiyya

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da cewa ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin 2026, inda ta ce za a fara dawo da maniyyata gida daga ranar 3 ga watan Yuni.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta bayyana cewa jirgi na ƙarshe ya tashi da ƙarfe 10:44 na safe daga filin jirgin saman Gusau a Jihar Zamfara, ɗauke da maniyyata zuwa Saudiyya ta hannun kamfanin Max Air.

NAHCON ta ce aikin jigilar maniyyatan ya fara ne tun ranar 3 ga watan Mayu, kuma an kammala jigilar a yau Alhamis 21 ga watan Mayu, 2026, a cikin kwanaki 18 kacal tare da jirage 98.

A cewar hukumar, Najeriya ta samu guraben aikin Hajji 50,000 a bana, ciki har da guraben da aka ware wa kamfanonin yawon Hajji masu lasisi da jami’an gudanarwa. Daga cikin adadin, an yi nasarar jigilar maniyyata 38,888 na gwamnati zuwa ƙasar Saudiyya.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa wasu daga cikin maniyyatan ba su samu damar tafiya ba sakamakon matsalolin rashin lafiya da kuma rasuwar wasu bayan an gama musu takardun biza.

Ready to PlayDala FM88.5 FM