Koma Labarai
Shari'a

Babbar kotun jaha a Kaduna ta sanya rana don fara sauraren shaidu a kan zargin kisan kai, sai dai wanda ake zargi yana hannun beli

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Babbar kotun jaha a Kaduna ta sanya rana don fara sauraren shaidu a kan zargin kisan kai, sai dai wanda ake zargi yana hannun beli

Babbar Kotun jaha mai zamanta a Dogarawa da ke jihar Kaduna, ta sanya ranar 16 ga wannan watan na Yuli, domin ci gaba da sauraron shaidu a ƙunshin tuhumar da gwamnatin Kaduna ta ke yi wa wani matashi mai suna Salmanu Lawan.

Ana zargin Salmanu Lawan ne da laifin kisan kai laifin da ya saɓa da sashi na 221 na penal code.

Ƙunshi zargin ya bayyana cewar a ranar 24/8/2025 wanda ake ƙara ya yi amfani da Adda ya sari wani mutum mai suna Abdurrahaman Bello a kansa, kuma bayan ya yi kwana ɗaya a asibiti ya rasu.

A zaman kotun na ranar Laraba 1 ga Yuli, 2026, masu ƙara sun zo da shaidun su amma lauyan gwamnati bai zo ba, a don haka kotun ta sanya ranar 16 ga wata don ci gaba.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta sanya rana don fara sauraren shaidu a kan zargin kisan kai, sai dai wanda ake zargi yana hannun beli.

Ready to PlayDala FM88.5 FM