Koma Labarai
Shari'a

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke rijistar jam'iyyar NDC a Najeriya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke rijistar jam'iyyar NDC a Najeriya

Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi, ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Kamfanin dillancin labarai na NAN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, ya ruwaito cewa Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke hukuncin ne ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa dole ne a bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar kare kansu kafin a yanke hukunci kan shari’ar.

Mai shari’ar ya amince da buƙatar jam’iyyar Peace Movement Party PMP, yana mai cewa jam’iyyar tana daga cikin waɗanda shari’ar ta shafa, ya ce hukuncin da aka yanke a watan Disambar 2025 ya saɓa wa kundin tsarin mulki domin an yanke shi ba tare da sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba.

Kotun ta kuma umarci a mayar da komai yadda yake kafin hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, har sai an sake sauraron shari’ar gaba ɗaya, haka kuma, ta ce an ɓoye wasu muhimman bayanai a lokacin shari’ar farko, lamarin da ya sa aka soke hukuncin.

Bugu da ƙari, kotun ta umarci a sake fara sauraron shari’ar daga farko tare da haɗa INEC, PMP da kuma NDC a matsayin ɓangarorin da za su halarta domin a tabbatar an yi adalci ga kowa.

Lauyan PMP, Chikezie Ekeocha, ya bayyana cewa sun garzaya kotu ne bayan sun gano cewa tambarin da aka yi wa NDC rajista da shi ya yi kama da wanda PMP ta gabatar wa INEC tun kafin fara shari’ar, kamar yadda kafar DCL Hausa ta ruwaito.

Ya ce hukuncin yana nufin an soke duk wani mataki da INEC ta ɗauka bisa tsohon hukuncin, ciki har da ba wa NDC takardar rajista da saka sunanta cikin bayanan hukumar, har sai an kammala sabon sauraron shari’ar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM