Koma Labarai
Iftila'i

Harin ƴan ƙwacen waya ya yi sanadiyyar mutuwar Yaya da ƙanin sa a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Harin ƴan ƙwacen waya ya yi sanadiyyar mutuwar Yaya da ƙanin sa a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta bayyana cewa, wasu matasa, ƴan ɗaki ɗaya, Sadiq Isyaku da Auwalu Isyaku, sun rasu a wani kudiddifi da ke unguwar Kureƙen Sani a ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, jami'in hulda da jama'a na hukumar a Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 9 ga watan Maris, 2026.

Sanarwar ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, bayan da hukumar ta karɓi kiran gaggawa daga wani Muhammad Abba, inda ya shaida musu cewa yaran su biyu sun fada a cikin ruwan.

A cewar sa, "Bayan da aka sanar da mu ne jami'an hukumar mu suka garzaya wajen inda su ka yi kokarin ceto yaran, sai dai aka fito da su ba da motsi, daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwar su, in ji Saminu.”

Har ila yau, ya kuma ce tuni aka miƙa gawarwakin matasan zuwa ga mahaifin su a Unguwa Uku.

A cewar Abdullahi, binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa yaran sun faɗa ruwan ne domin tsira daga ƴan ƙwacen waya da suke bin su za su yi musu ƙwace a lokacin.

Ready to PlayDala FM88.5 FM