Koma Labarai
Iftila'i

Fiye da ‘yanbindiga 150 ne suka nutse bayan kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Fiye da ‘yanbindiga 150 ne suka nutse bayan kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

Aƙalla ‘yanbindiga sama da 150 sun mutu sakamakon nutsewa bayan wani kwale-kwale da ke dauke da su ya kife a yankin Sabon Gida da ke Jihar Sokoto, kamar yadda Zagazola Makamai ya rawaito.

Majiyoyin yankin sun shaida wa Zagazola Makamai cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar, lokacin da jirgin ruwan da ke dauke da dimbin ‘yanbindiga dauke da makamai ya kife yayin da suke kokarin tsallaka wani tafki a yankin.

A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar na tafiya ne a cikin yawa kafin kwale-kwalen ya kife ba zato ba tsammani, lamarin da ya jefa dukkan fasinjojin cikin ruwa.

A cewar wata majiya, “Bayanan farko sun nuna cewa da dama daga cikinsu ba su iya iyo ba, wanda ya haddasa yawan mace-mace."

Rahotannin farko sun nuna cewa babu wanda ya tsira daga cikin fasinjojin, sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro zuwa lokacin hada wannan rahoto, kamar yadda kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito.

Idan aka tabbatar da faruwar lamarin, ana sa ran hakan zai yi matukar tasiri ga kungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a wasu sassan yankin Arewa maso Yamma.

Ready to PlayDala FM88.5 FM