Mutane uku sun mutu a hatsarin manyan motoci da ya faru a Kano

Aƙalla mutane uku ake kyautata zaton sun rasu a cikin motar ɗaukar Lemo, bayan da ta daki motar Tirela a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura.
Hatsarin dai ya faru ne da safiyar yau Litinin 9 ga watan Maris, 2026, inda sikiyarin babbar motar ɗaukar Lemon ya ƙwace ta daki wata motar Tirela, da da ke tsaye a gefen hanya bayan da ta samu matsala.
Wani shaidar gani da ido mai suna Zailani Umar Imawa, ya ce suna zaune suka ga motar ɗaukar Lemon ta daki babbar motar Tirela, ko da suka ƙarasa gurin suka tarar mutane uku da ke cikin motar lemon suna cikin mawuyacin hali.
Ya ce sun tarar biyu daga cikin mutanen basa iya motsa jikin su, inda ɗayan ke neman ɗaukin a taimaka masa, bayan da jami'an Hukumar kiyaye aukuwar haɗura suka kai su asibiti ne aka tabbatar da rasuwar mutanen uku.
Sai dai har lokacin kammala haɗa rahoto ba a tabbatar da samun waɗanda suka san masu babbar motar dakon Lemon ba.
