Iftila'i: Wata mota ta faɗa cikin wani babban rami a Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Wata mota ta faɗa cikin wani babban rami da ke kan hanyar Unguwar Maƙera zuwa Kiru a Jihar Kano, da ke arewacin Najeriya.
Shaidar gani da ido Yahaya Akilu daga Garin Kiru a Kano, ya ce motar na kan hanyarta ne daga Jihar Legas zuwa Garin Kiru lokacin da hadarin ya faru a ranar Laraba 11 ga watan Maris, 2026.
Rahotanni sun bayyana cewa babu asarar rai a faɗuwar motar, sai dai wasu daga cikin fasinjojin motar sun samu raunuka, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.


