Gwamnan Kano Abba Kabir ya taya Kwankwaso murnar cika shekaru 70.

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya taya tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Tsaro, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, murnar cika shekara 70 da haihuwa a duniya.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Laraba 21 ga watan Oktoba, 2026.
Gwamnan ya bayyana zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso a matsayin wata dama ta tunawa da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kano da Najeriya.
Abba Yusuf ya yaba da rawar da Kwankwaso ya taka wajen bunƙasa siyasa, inganta shugabanci da samar da ababen more rayuwa a jihar.
Ya ce shekarun da tsohon gwamnan ya shafe yana hidimar al'umma sun taimaka wajen faɗaɗa harkokin dimokuraɗiyya da ci gaban jihar.
Gwamnan ya kuma roƙi Allah Ya ba Kwankwaso lafiya, tsawon rai da ƙarin ƙarfi domin ci gaba da bayar da gudunmawa ga ci gaban Kano da Najeriya.
Haka kuma, ya yi masa fatan samun ƙarin shekarun zaman lafiya da farin ciki yayin da yake bikin cika shekara 70 da haihuwa.



