Koma Labarai
Labarai

Gwamnan Kano ya nemi afuwar ƴan kasuwar Singa kan jinkirin basu tallafin gobara.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan Kano ya nemi afuwar ƴan kasuwar Singa kan jinkirin basu tallafin gobara.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nemi afuwar ’yan kasuwar Singa da gobara ta shafa bisa jinkirin isar musu da tallafi, yayin da aka raba musu kayayyakin agaji da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayar a yau.

Wakilinmu, Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewa, Babban Sakataren Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Jihar Kano, Abdulmuminu Musa Ado, wanda ya wakilci Kwamishinan ma’aikatar, Muktari Ishaq Yakasai, ne ya bayyana hakan a taron rabon tallafin da aka gudanar a Kano.

Babban Jami’in NEMA na shiyyar Kano da Jigawa, Nura Abdullahi, ya ce kayayyakin tallafin sun haɗa da na gini da kuma kayan masarufi. A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Isyaku Abdullahi Kubarachi, ya gargaɗi ’yan kasuwar da su guji sayar da kayayyakin da aka ba su.

Da yake jawabi a madadin ’yan kasuwar, Shugaban Ƙungiyar Kasuwar Singa da Kewaye, Alhaji Musa Ibrahim Nabanki, ya gode wa gwamnatocin jiha da tarayya, tare da roƙon a gaggauta raba musu tallafin kuɗi naira biliyan takwas da aka yi musu alkawari.

Taron ya samu halartar ’yan kasuwar da wadan da abun ya shafa da sauran ƙungiyoyin agaji.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM