Talauci ne ke tilasta Almajirai fita bara kan tituna a Najeriya – Sarkin Musulmi
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya ɗora alhakin fitar da yara Almajirai ke yi kan tituna suna bara a kan talauci, inda ya bayyana cewa mafi yawansu suna da sha’awar neman ilimi,
Sai dai ya ce rashin kuɗi da kayan masarufi ne ke hana su samun damar yin hakan.
Sarkin ya bayyana hakan ne a garin Gombe, yayin babban taron ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar Barewa (Barewa Old Boys Association – BOBA), inda ya halarci taron a matsayin shugaban bikin.
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta ɗaukar matakan magance talauci da kuma ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.



